'Yan majalisar sun kada kuri'ar amincewa 412 a kan 202 da suka ki, inda aka samu bambancin kuri'u 210, da nufin neman amincewar EU na jinkirta ficewar kasar zuwa ranar 30 ga watan Yuni.
Sakamakon na nufin bukatar Birtaniya ga EU da ta jinkirta yarjejeniyar ficewar kasar daga ranar 29 ga watan Maris da aka sanya a baya.
Ana ganin sakamakon a matsayin nasara ga gwamnatin Birtaniya da ta gabatar da kudurin, yayin da 'yan majalisar kuma suka ki amincewa da kudurin Jam'iyyar adawa ta Labour ta sauya dabarun kasar na ficewa daga Tarayyar.(Fa'iza Mustapha)