A kuri'ar da mambobin majalisar 312 zuwa 308 suka kada, sun gaza amincewa da bukatar, wanda aka kada kuri'ar da misalin karfe 19:00 agogon GMT. Sakamakon baya bayan nan ya nuna cewa gwamnatin Birtaniya ta gaza samun galaba kan wannan bukatar.
Majalisar dai ta kada kuri'ar ne game da ko Birtaniyan za ta iya ficewa daga tarayyar Turai ba tare da cimma wata yarjejeniya ba kafin cikar wa'adin ficewar a ranar 29 ga watan Maris.
A ranar Talata da dare, mambobin majalisar dokokin 391 suka kada kuri'ar, mambobi 242 sun ki amincewa da bukatar, inda suka rinjayi mambobi 149, wajen yin watsi da sabuwar bukatar ficewar kasar Birtaniyan wadda aka yi wa kwaskwarima wadda firaiminista May ta gabatar, lamarin da ya haifar da rudani game da shirin ficewar kasar daga tarayyar Turai. (Ahmad Fagam)