Majalisar dokokin Burtaniya ta yi watsi da yarjejeniyar ficewar kasar daga EU da May ta gabatar
Majalisar dokokin Burtnaiya ta sake kada kuri'ar kin amincewa da babban rinjaye kan yarjejeniyar ficewar kasar daga kungiyar tarayyar Turai da firaministar kasar Theresa May ta gabatar. Kuri'ar da 'yan majalisar suka kada a jiya Talata, ita ce, mafi rinjaye tun wadda majalisar ta kada a watan Janairu, abin da ke kara nuna rashin tabbas game da yadda kasar za ta fice daga kungiyar ta EU.
'Yan majalisa 391 ne dai suka kada kuri'ar kin amincewa da yarjejeniyar ficewar kasar daga EU da aka yiwa gyaran fuska da firaministar ta gabatar, yayin da 'yan majalisa 242 suka amince da ita, wannan wata babbar koma baya ce, bayan ta ranar 15 ga watan Janairu, lokacin da 'yan majalisar suka yi watsi da yarjejeniyar da May ta gabatar, inda aka samu tazarar kuri'u 230 kan kunshin yarjejeniyar.(Ibrahim)