Firaministar kasar Birtaniya Theresa May ta ce, idan majalisar wakilan kasar ba ta zartas da yarjejeniyar ficewar kasar daga kungiyar Tarayyar Turai wato EU a wata mai zuwa ba, kuma ba a yarda da ficewar kasar daga EU ba tare da wata yarjejeniya ba, za a bar majalisar wakilan kasar ta kada kuri'a kan ko za a jinkirta ficewar kasar daga EU ko a'a.
Madam May ta fadi haka ne jiya Talata a majalisar wakilan kasar, inda ta kuma yi alkawarin cewa, za a kada kuri'a karo na 2 kan yarjejeniyar ficewar kasar daga EU a majalisar wakilan kasar kafin ranar 12 ga watan Maris. Ta ce idan ba a cimma yarjejeniyar ba, to a kashegari za a kada kuri'a kan ko Birtaniya za ta fice daga EU ba tare da wata yarjejeniya ba. Madam May ta kara da cewa, idan majalisar wakilan kasar ba ta yarda da barin EU ba tare da wata yarjejeniya ba, za ta ci gaba da jefa kuri'a kan ko za a jinkirta ficewar kasar daga EU ko a'a. Firaministar ta jaddada cewa, ba ta son ganin an dage batun barin EU a ranar 29 ga watan Maris. (Tasallah Yuan)