An gudanar da taron rufe zama na 2, na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na 13 a yau da safe, agogon birnin Beijing.
Shugaban kasar Sin, Xi Jinping da sauran shugabannin kasar ne suka halarci taron, a babban dakin taron al'ummar kasar Sin dake nan birnin Beijing
Mambobin majalisar sun amince da dokar zuba jari na bai daya ta baki na farko a kasar, wadda ta nuna yunkurin kasar na shiga wani sabon mataki na zurfafa bude kofa.
Sun kuma amince da kudure-kudure kan rahoton ayyukan gwamnati da kuma rahoton aiki na kwamitin kolin majalisar, da kotun koli na jama'ar kasar da hukumar koli mai gabatar da kararraki da gudanar da bincike ta kasar.
Baya ga haka, wakilan sun amince da rahoton tsare-tsaren tattalin arziki da na ci gaban al'umma da kuma kasafin kudin kasar da na yankuna. Har ila yau, sun amince da murabus din shugaban kwamitin kolin majalisar, Zhang Rongshun. (Fa'iza Msuatpha)