Wang Yang, shugaban majalisar CPPCC, ya furta a wajen bikin rufe taron cewa, bana ake cika shekaru 70 da kafa jamhuriyar Jama'ar kasar Sin. kuma cikin shekaru 70 da suka gabata, majalisar CPPCC ta yi kokarin samar da gudunmowa ga ayyukan kafa kasar Sin, da gina kasar, da binciken hanyar gudanar da gyare-gyare a kasar, gami da kokarin cimma burin kasar na samun ci gaban tattalin arziki da kyautata zaman al'umma. Sa'an nan a wannan sabon zamanin da ake ciki, majalisar za ta iya taka rawar gani a karin fannoni, kana akwai karin nauyin dake wuyanta. Saboda haka dole ne majalisar ta tsaya kan kokarin sauke nauyin da aka dora mata, ta yadda za ta samu damar gudanar da harkokinta yadda ake bukata, da baiwa jama'ar kasar cikakkiyar damar ba da shawara kan harkokin siyasa.
An kwashe yini 11 wajen gudanar da taron shekara-shekara na majalisar CPPCC na wannan karo, inda 'yan majalisar fiye da 2100 dake wakiltar jam'iyyu da kungiyoyi daban daban, da al'ummomin kasar daban daban, gami da masu sana'o'i daban daban na kasar Sin, suka hallara. (Bello Wang)