in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin CMG ya yi amfani da fasahohin 5G da 4K a zauren watsa labarai masu alaka da tarukan majalissun kasar Sin
2019-03-12 11:39:19 cri

A yayin da ake gudanar da muhimman tarukan shekara-shekara na majalissun kasar Sin guda 2, wato taron NPC da CPPCC, babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG ya yi amfani da wasu sabbin fasahohin sadarwa da na watsa labaru wajen gabatar da manufofi da ra'ayi na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, gami da ra'ayoyin 'yan majalisun.

Don gabatar da bayanai masu alaka da tarukan majalissun kasar Sin, babban gidin rediyo da telabijin na kasar Sin CMG ya yi amfani da fasahar sadarwa ta 5G don tura hotunan bidiyo masu matukar inganci na 4K, wanda ya kasance karo na farko a duniya. Sa'an nan don sanya 'yan majalisun su fahimci wadannan sabbin fasahohi, CMG ya kebe wasu wurare a zauren babban dakin taron jama'ar kasar Sin, da cibiyar watsa labarai ta tarukan majalisun 2, gami da wuraren da 'yan majalisun suke zama, don nuna fasahar nuna hotunan bidiyo masu ingancin gaske na 4K, wadanda aka turo su ta fasahar sadarwa ta 5G.

Ban da wannan kuma, a wajen cibiyar watsa labarai ta fasahar 5G ta CMG, an yi amfani da fasahohi na AI, da masu sarrafa alkaluma, wajen tsara hotunan 4K, da bidiyon VR, sa'an nan an tura su zuwa wurare daban daban nan take.

Har ila yau, bisa wani dandalinsa na hada fasahohin watsa labaru daban daban, CMG ya yi hadin gwiwa tare da cibiyoyin tsara bayanai da aka kafa su a gundumomi fiye da 500, don tara ra'ayoyin jama'a, ta yadda aka sanya kafar watsa labarai data shafi matakai daban daban, gami da baiwa kowa damar bayyana ra'ayinsa.

Banda haka kuma, babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG ya yi amfani da kafofinsa masu alaka da bidiyo da sautin murya wajen watsa labarai ta fasahohin zamani daban daban, ta yadda aka hada shirye-shiryen CCTV, da CNR, da CRI, da sauran kafofin watsa labaru dake karkashin CMG.

Kafin haka, a ranar 28 ga watan Fabrairun bana, CMG ya samu nasara wajen gwada fasahar hada shirye-shiryen hotunan bidyo masu inganci na 4K, gami da tura su ta fasahar sadarwa ta 5G, lamarin da ya shaida cewa, CMG ya iya sarrafa shirye-shiryen bidiyo masu ingancin gaske a wurare daban daban gami da turasu cikin sauri. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China