in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta sanya hannu kan doka zubar jari ta ketare
2019-03-15 09:55:45 cri
A yau Jumma'a ne, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta sanya hannu kan dokar zuba jari ta ketare, a daidai gabar da majalisar ke kammala taronta na shekara-shekara na bana.

Galibin wakilan da suka halarci rufe zama na biyu na taron majalisar wakilan karo na 13, sun goyi bayan dokar.

Sabuwar dokar da ta baiwa baki iznin zuba jari a cikin kasar, ta tanadi izinin shiga, da yayata, kare da kuma kula da jarin da baki 'yan kasashen waje za su zuba a kasar kamar yadda dokar ta tanada.

Manufar sabuwar dokar dai, ita ce, inganta daidaito kan manufofin zuba jarin waje da tabbatar da cewa, an baiwa kamfanonin gida da na wajen kulawa iri daya bisa doka da damar yin takara a kasuwa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China