Ministan harkokin kudi da tsare-tsare na kasar Philip Mpango, ya ce za a kashe galibin kasafin kudin ne kan inganta ababen more rayuwa, kamar layukan dogo da tituna da samar da wutar lantarki a yankunan karkara.
Philip Mpango, ya bayyana haka ne lokacin da yake gabatar da daftarin manufar ciyar da kasar gaba da na kasafin kudin 2019/2020 ga mambobin majalisar dokokin kasar a birnin Dodoma.
Ministan ya ce kasafin zai ci gaba da mayar da hankali ne kan habaka ayyukan masana'antu domin samar da ayyukan yi da inganta walwalar jama'a.
Ya ce za kuma su tabbatar da an yi amfani da kudin gwamnati yadda ya kamata ta hanyar zuba su a bangaren ababen more rayuwa da hidimomin al'umma, a kokarin gaggauta samun ci gaba a kasar.
Ya kara da cewa, gwamnati ta kuma kuduri niyyar kara yaki da cin hanci da wawurar dukiyar al'umma da kuma inganta yanayin zuba jari a kasar. (Fa'iza Mustapha)