in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tanzania na fuskantar babbar barazanar barkewar annobar Ebola
2018-08-22 10:35:19 cri
Wata babbar jami'ar kasar Tanzania ta tabbatar a ranar Talata cewa, kasar tana fuskantar babban hadari na yiwuwar barkewar annobar Ebola, bayan da cutar ta kashe wasu mutane 50 daga cikin majinyata 91 a kasar jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (DRC) dake makwabtaka da Tanzania.

Ummy Mwalimu, ministar lafiya ta kasar Tanzania, ta fadi hakan a gaban manema labaru a birnin Dar es Salaam, cibiyar tattalin arzikin kasar, inda ta ce dalilin da ya sa aka fadi haka shi ne domin alkaluman da hukumar lafiya ta duniya WHO ta samar sun sheda cewa, sabuwar barkewar cutar Ebola a kasar DRC ana samunta ne a wasu yankunan da suke da matukar kusanci da kasar Tanzania, wadanda suka hada da arewacin Kivu, da Ituri.

Ministar ta kara da cewa, yanzu dukkan kasashe makwabtan kasar DRC na fuskantar barazanar yiwuwar barkewar cutar Ebola, domin yankin na arewacin Kivu na kasar ya hada kan iyaka guda da kasar Uganda, sa'an nan mutane da yawa na gudun hijira daga yankin zuwa sauran kasashen da suka hada da Uganda da Rwanda.

Sai dai a cewar ministar, har yanzu ba a samu wanda ya kamu da cutar Ebola ba tukuna a cikin kasar ta Tanzania. Amma ta jaddada bukatar daukar matakan rigakafi don magance samun irin annobar da ake fuskanta a kasar ta DRC. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China