Samia wadda ta yi wannan kira, jim kadan da rantsar da sabbin masu shari'a 3 a birnin Arusha, ta ce wasu hukumomin kungiyar ta AU, kamar kotun lura da hakkokin bil Adama ta AFCHR, sun shiga wani yanayi sakamakon karancin kudaden gudanarwa.
Jami'ar ta kara da cewa, ya dace ko wace kasa ta gabatar da tallafin ta a kan lokaci, ganin cewa kasashe da dama sun sanya hannu kan yarjejeniyar samar da tallafin kudade, wadanda za su ba da damar ci gaba da ayyuka, maimakon dogaro da hukumomin wajen nahiyar dake samar da taimako.
Uwargida Samia ta ce gwamnatin Tanzania, wadda daya ce cikin sassa da suka sanya hannu kan yarjejeniyar kafa kotun, ta alkawarta ci gaba da hadin gwiwa domin cimma nasarar ayyukan ta. (Saminu)