Ministan cikin gidan kasar Kangi Lugola, shi ne ya bayyana hakan a jiya Lahadi, yayin ganawa da wakilin UNHCR na Tanzania Chansa Kapaya. Jami'an biyu sun tattauna game da batutuwan da suka shafi 'yan gudun hijira, da yadda Tanzania za ta ci gaba da hadin gwiwa da hukumar ta MDD, karkashin tanajin dokoki da ka'idojin kasa da kasa.
Mr. Lugola ya ce mawuyaci ne Tanzania ta cimma nasara a fannin tallafawa, da tsugunar da 'yan gudun hijira, ba tare da hadin gwiwar UNHCR ba. (Saminu Hassan)