in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Uku daga cikin daliban jami'ar Tanzaniya sun lashe gasar kamfanin Huawei na fasahar zamani
2018-12-06 13:15:24 cri
Firaiministan kasar Tanzaniya Kassim Majaliwa, a jiya Laraba ya gabatar da takardun sheda ga dalibai 3 na jami'ar kasar wadanda suka yi nasara a gasar kwarewa kan fasahar sadarwa ta zamani ICT wanda kamfanin Huawei ya shirya a kudancin Afrika na shekarar 2018/2019.

Huawei ya sanar da cewa, wadanda suka samu nasarar za su hadu da sauran dalibai daga kasashen kudancin Afrika domin yin wata gasar da za ta gudana a watan Fabrairun shekara mai zuwa, wanda za'a gudanar a kasar Afrika ta kudu, daga bisani kuma a gudanar a kasar Sin idan daliban suka samu nasara a zagaye na biyu.

Majaliwa ya ce, Huawei ya kasance daya daga cikin manyan kamfanonin duniya wadanda ke sahun gaba ta fannin ci gaban fasahar sadarwa ta zamani wato (ICT).

Firaiministan ya kara da cewa, wannan gasa da aka shirya ta zo ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar Tanzania take da matukar bukatar samun kwararru a fannin ICT domin su taimakawa kasar ta gabashin Afrika wajen bunkasa ci gaban masana'antunta. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China