Taron wanda aka gudanar a babbar cibiyar taron MDD dake Addis Ababa inda aka girmama ma'aikatan MDDr 19 wadanda suka hallaka a hadarin jirgin saman samfurin Boeing 737-8 MAX a kusa da garin Bishoftu, mai tazarar kilomita 45 daga Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha a ranar Lahadi.
"Rana ce mai cike da bakin ciki," Vera Songwe, babbar sakatariyar hukuma mai kula tattalin arzikin Afrika ta MDD wato (ECA), ta bayyana hakan ne a lokacin taron zaman makokin.
Wakilan dukkanin hukumomin MDD sun hallara a kasar Habasha domin daga tuta don karrama mamatan a harabar ofishin hukumar ta ECA a jiya Litinin. (Ahamd Fagam)