in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kama 'yan kasar Habasha 60 bisa zargi hannu a tashin hankalin kabilanci
2019-01-18 21:16:08 cri
Mahukuntan kasar Habasha sun sanar a yau Jumma'a cewa, sun kama wasu mutane 60 bisa zargin da ake musu da hannu a tashe-tashen hankulan kabilancin da suka faru a yankin yammacin kasar.

Wata sanarwa da hukumar sadarwar yankin Oromia ta fitar ta bayyana cewa, ana zargin mutane 60 din da aka kama ne, da kitsawa da farma fararen hula a yankunan jihohin Benishangul Gumuz da Oromia dake kan iyaka.

Sanarwar ta ce, an kama mutanen ne a kwanakin baya, biyon bayan wani hadin gwiwar hukumomin tsaron yankin da na tarayya.

A 'yan shekarun nan, yankunan dake kan iyakokin jihohin biyu dai sun fuskanci munanan tashin hankali tsakanin kungiyoyin kabilu daban-daban dake zaune a kan iyakokin. Tashin hankalin dai ya faru ne sakamakon neman mallakar filaye da albarkatu.

Rahotannin baya-bayan da ofishin kula da harkokin jin kai na MDD ya fitar na cewa, tashin hankalin ya yi sanadiyar rayukan mutane da dama, baya ga kimanin mutane 255,000 da suka rasa matsugunansu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China