in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Jirgin saman kasar Habasha zai kara yawan zirga-zirga a Guangzhou na kasar Sin
2019-03-04 11:28:12 cri

Kamfanin jirgin sama na kasar Habasha wato Ethiopian Airlines, na shirin rubanya zirga-zirgarsa a birnin Guangzhou na kasar Sin.

Manajan Daraktan kamfanin mai kula da harkokin kasashen waje, Esayas Woldemariam, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, jirgin na shirin zuwa Guangzhou sau biyu a rana maimakon sau daya da yake zuwa.

A yanzu, jirgin na zuwa biranen Guangzhou da Beijing daga birnin Addis Ababa ne sau daya a rana, sannan ya je Chengdu sau 3 a ko wane mako.

Esayas Woldermariam, ya ce daga watan Oktoban 2019, suna shirin rubanya zirga zirgar jirginsu a Guangzhou, domin biyan bukatun fasinjojinsu dake karuwa.

Har ila yau, ya ce Kamfanin jirgin saman na shirin fara zuwa wasu karin wurare a kasar Sin, domin saukaka dangantakar dake kara kulluwa tsakanin kasashen Afrika da Sin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China