in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Habasha da Kenya sun kaddamar da rukunin masana'antu wanda Sin ta gina
2019-03-03 17:00:13 cri

Firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed, da shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, a jiya Asabar sun kaddamar da rukunin masana'antun Debre Birhan wanda kasar Sin ta gina, a jihar Amhara dake arewacin kasar Habasha.

Kamfanin gine gine na CCCC na kasar Sin shi ne ya gina rukunin masana'antun na Debre Birhan wanda ya lashe kudi sama da dala miliyan 71, ana sa ran aikin zai samar da guraben aikin yi sama da 1,000 ga mutanen kasar Habasha.

Fadin yankin da aka gina ya kai hekta 75, rukunin masana'antun na Debre Birhan ya kunshi bangarorin masana'antu 8 wadanda za su janyo hankalin masu zuba jari.

Shugaban kasar Kenyan ya yabawa firaministan kasar Habasha sakamakon irin jajurcewarsa na kokarin habaka kafa rukunin masana'antu don bunkasa tattalin arzikin kasar wadanda suka kawo sauye-sauye ga cigaba kasar ta Habasha ciki har da aikin rukunin masana'ntun Debre Birhan, in ji wata sanarwa daga ofishin firaministan kasar Habashan.

Da yake jawabi ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan baya, Lelise Neme, babban jami'in hukumar gudanarwar rukunin masana'antun kasar Habasha (IPDC), ya ce kasar Habasha tana da burin kaddamar da rukunin masana'antu 6 da suka hada da na Debre Birhan, kafin karshen shekarar 2018/19, a watan Yuli.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China