in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar 'yan gudun hijira ta MDD ta yi maraba da gyara dokar 'yan gudun hijirar da Habasha ta yi
2019-01-19 16:05:46 cri
Ofishin babban jami'in kula da 'yan gudun hijira na MDD (UNHCR), ya yi maraba da tarihin da kasar Habasha ta kafa na fitar da sabuwar dokar da zata baiwa 'yan gudun hijira damar cin moriyar muhimman abubuwan more rayuwa da kuma ba su damar shiga harkokin yau da kullum a tsakanin al'umma.

A ranar Alhamis majalisar dokokin kasar Habashan ta amince da yi wa dokar 'yan gudun hijira ta kasar kwaskwarima, wannan shi ne cigaba mafi girma da aka samu game da manufofin da suka shafi 'yan gudun hijira a Afrika, kamar yadda hukumar UNHCR ta sanar a jiya.

Sabuwar dokar ta amincewa 'yan gudun hijirar mallakar shedar iznin yin aiki a kasar, da samun damar yin ilmin firamare, da mallakar lasisin tuki, da yin rejistar al'amurra na rayuwa kamar takardun haihuwa da na aure, da kuma amfani da harkokin kudade a kasar kamar bankuna.

Matakin da Habashan ta dauka na gyaran fuska kan dokokin 'yan gudun hijirar ya zo ne bayan da babban taron MDD ya amince da wata yarjejeniyar kasa da kasa game da batun 'yan gudun hijirar a ranar 17 ga watan Disambar 2018.

A halin da ake ciki Habasha tana karbar bakuncin 'yan gudun hijira kimanin 900,000, daga makwabtan kasashe da suka hada da Sudan ta kudu, Somalia, Sudan da Eritrea, da kuma wasu 'yan kadan daga cikin 'yan gudun hijirar Yemen da Syria, inji hukumar UNHCR.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China