in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane da dama sun bace sakamakon fashewar tashar iskar gas a kudancin Najeriya
2019-03-03 15:48:10 cri

Mutane da dama sun bace a yankin Niger Delta dake kudancin Najeriya sakamakon fashewar tashar iskar gas, hukumomin yankin sun tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar.

Majalisar masarautar Nembe dake yankin ta ce, lamarin ya afku ne a ranar Jumma'a a yankin Nembe dake jihar Bayelsa a kudancin kasar, yayin da mazauna yankin da suka hada da mata da kananan yara suka tsere don neman tsira da rayuwarsu.

Nengi James-Eriworio, kakakin majalisar masarautar Nembe, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kimanin yankuna 6 ne matsalar ta shafa. Aikin kamun kifi shi ne babbar hanyar samun kudaden shigar mutanen yankin Nembe.

"Wannan ibtila'i ya haifar da mummanar illa wajen gurbata yanayin iskar da ruwa a yankin," inji James-Eriworio.

Kawo yanzu ba'a gano musabbabin fashewar ba. Kuma ba'a bayyana wadanda suka jikkata to suka mutu a sanadin hadarin ba.

Sai dai, wasu rahotanni sun ce kimanin mutane 60 ko sama da haka ne suka bace, wani babban jami'in hukumar tsaron jihar Bayelsa shi ne ya bayyana hakan ga Xinhua ta wayar tarho a jiya Asabar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China