Kakakin hukumar 'yan sandan jihar ta Zamfara, Mohammed Shehu, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa an kaddamar da harin ne kan kauyen Kware a karamar hukumar Shinkafi inda maharan suka shafe sa'o'i da dama da safiyar ranar Litinin. Maharan dai sun bude wuta ne kan jama'a mazauna kauyen sannan suka cinna wuta a gidajensu.
Daruruwa baburan hawa ne maharan suka yi amfani da su inda suka yi wa kauyen tsinke, kamar yadda wasu mazauna garin suka bayyana.
Sai dai mazauna garin sun ce adadin wadanda suka mutu ya kai 35, kana wasu mazauna kauyen da dama sun tsere daga kauyen. Sannan akwai wadanda suka bace har yanzu ba'a ji duriyarsu ba. (Ahmad Fagam)