in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
INEC ta ayyana Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar
2019-02-27 13:29:49 cri

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya wato INEC ta ayyana shugaba Muhammadu Buhari a matsayi wanda ya lashe zaben shugabancin kasar da ya gudana a ranar Asabar din da ta gabata.

Shugaban hukumar Mahmod Yakubu ya ce, Buhari dan takarar jam'iyyar APC mai mulkin kasar ya samu kuru'u 15,191,847 wato kaso 55.6 cikin 100 a kuru'u 27,324,583 da aka kada a lokacin zaben. Yayin da abokin hamayyarsa Atiku Abubakar na jam'iyyar adawa ta PDP ya samu kuru'u 11,262,978 ko kuma kaso 41.2 cikin 100 na kuru'un da aka kada.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China