in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar barkewar zazzabin lassa a Nijeriya ya kai 83
2019-03-02 15:14:54 cri
Cibiyar takaita yaduwar cutuka ta Nijeriya, ta ce adadin wadanda suka mutu sanadiyyar barkewar zazzabin lassa a kasar ya kai 83.

Wata sanarwa da cibiyar ta NCDC ta fitar a jiya, ta ce adadin ya dauki kaso 21.8 na wadanda suka mutu sanadiyyar cutar, tun bayan barkewarta a cikin watan Junairu.

Jihohi a kalla 21 daga cikin 36 ne suka fuskanci barkewar cutar mai sanya matsanancin zazzabin. An samu sabbin wadanda suka kamu da cutar ne tsakanin ranar 18 zuwa 24 ga watan Fabreru.

A cewar cibiyar, kawo yanzu, mutane 1,279 ne aka zargin sun kamu da cutar a fadin kasar. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China