A wajen taron manema labarai da aka yi yau na zaman taro na biyu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13, Wang ya bayyana cewa, kasar Sin za ta shiga cikin jerin kasashen duniya dake yin kirkire-kirkire nan da shekara ta 2020, sa'annan, nan da shekara ta 2035, Sin za ta shiga cikin jerin kasashen dake kan gaba a fannin yin kirkire-kirkire, kafin daga bisani wato zuwa shekara ta 2050, Sin za ta zama kasa mai karfin yin kirkire-kirkire a duk fadin duniya.
Wang ya kuma kara da cewa, Sin za ta kara biyan bukatun mutanen da suke yin bincike da nazari a fannin kimiyya da fasaha, da samar da duk wani tabbaci ga aikin yin kirkire-kirkire a wannan fanni.(Murtala Zhang)