Yau Lahadi shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci zaman tattaunawar tawagar wakilan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta lardin Fujian, inda ya bayyana cewa, kasar Sin tana kokarin neman samun wata sabuwar hanya domin ingiza ci gaban huldar dake tsakanin bangarori biyu na zirin Taiwan, ya kara da cewa, ya kamata bangarorin biyu wato babban yankin kasar Sin da lardin Taiwan na kasar su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya da gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a da samar da makamashi, tare kuma da mayar da lardin Fujian a matsayin wuri mafi dacewa, inda 'yanuwa a Taiwan zasu kafa kamfanoni a kai.(Jamila)