Bisa kididdigar da bankin duniya ya yi, a cikin mutane 100 da suka kawar da talauci a duniya, guda 70 sun fito ne daga kasar Sin. Direktan cibiyar nazari kan kasar Sin ta kasar Nijeriya Charles Onunaiju ya yi tsokaci cewa, matakan yaki da talauci da Sin ta dauka suna da amfani kana masu dorewa ne, ana bukatar kasar Nijeriya ta koyi fasahohi da nasarorin da Sin ta samu wajen yaki da talauci a kauyuka, da sa kaimi ga canja tunanin manoma da bunkasa tattalin arzikin kauyuka, ta hakan manoma suna iya samun damar samun wadata da rike damar don samun bunkasuwa mai dorewa.
Masanin tattalin arzikin kasa da kasa na jami'ar Nairobi ta kasar Kenya Garrishon Ikiara ya bayyana cewa, Sin ta dauki kwararan matakai na yaki da talauci da bunkasa tattalin arziki, wadanda suka amfanawa jama'ar kasar, ya kamata kasashen Afirka su koyi fasahohi da nasarorin da Sin ta samu a fannoni daban daban. Kawar da talauci shi ne muhimmin burin da kasashen Afirka suke neman cimmawa da farko, ya zuwa yanzu bangarorin biyu sun yi hadin gwiwa a fannonin yaki da talauci da samun ci gaba. (Zainab)