A kwanakin baya, kamfanin Airbus ya shelanta fara amfani da cibiyar kirkiro sabbin fasahohin zamani da ya kafa a birnin Shenzhen na kasar Sin. Wannan cibiya tilo da kamfanin ya kafa a yankin Asiya, zai yi amfani da kwararru wadanda suke da ilmin kirkiro sabbin fasahohin zamani da wadanda suke hadin gwiwa da kamfanin a wurin, ta yadda zai iya kara karfinsa na kirkiro sabbin fasahohin zamani, har ma zai iya nazari da kuma fitar da sabon jirgin sama da zai biya bukatun da ake da su a kasuwar nan gaba.
Matakin da kamfanin Airbus ya dauka ya kasance kamar wani karamin bayani ne ga sabon zagaye na kara bude kofar kasar Sin ga ketare bisa matsayi mai inganci. Ko da yake yawan zuba jari da aka yi a tsakanin kasa da kasa ya ragu da 19% a shekarar bara, yawan jarin waje da aka zuba a kasar Sin a bara ya karu da 3%, har ma a bana, wannan adadi yana ta karuwa. Sabuwar kididdigar da ma'aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin ta fitar ta bayyana cewa, yawan jarin waje da kasar Sin ta yi amfani da su ya karu da 4.8% bisa makamancin lokacin a bara, sannan yawan jarin da 'yan kasuwar kasar Amurka suka zuba a kasar Sin ya karu da 124.6%, a yayin da yawan jarin da 'yan kasuwar kasar Holland suka zuba a kasar Sin ya karu da 95.6%.
Har yanzu, saurin farfadowar tattalin arzikin duniya yana ta raguwa, amma kasar Sin ba ta tsaya ko kadan ba, wajen kaddamar da sabon zagayen bude kofarta ga ketare domin tabbatar da samun ci gaba mai inganci. Wannan matakin da kowa ke gani shi ne, yanzu wakilan jama'a fiye da 2900 suna dudduba daftarin "dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa" a nan Beijing. Kasar Sin tana fatan wannan doka za ta iya karfafawa baki 'yan kasuwa gwiwar zuba jari a kasar, kare 'yancinsu bisa doka, da kuma kafa wani yanayin kasuwanci bisa doka da ya yi daidai da yanayin kasuwanci da ake ciki a sauran kasashen duniya, ta yadda za a iya ba da kariya ga kokarin kaddamar da sabon zagayen bude kofa ga ketare domin samun sabon ci gaba mai inganci.
A ganin shugaban kasar Sin Xi Jinping, tattalin arzikin kasar ya samu habaka a cikin shekaru 40 da suka wuce, duba da yadda take aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare. A nan gaba kuma, idan kasar Sin na son ci gaba da bunkasa tattalin arzikinta mai inganci kuma ta hanyar da ta dace, ya zama dole ta kara bude kofarta ga ketare. A shekaru biyar da suka shude, Sin ta yanke shawarar zurfafa yin kwaskwarima ga ci gaban harkokin zamantakewar al'umma, ciki har da gaggauta kyautata tsarin tattalin arziki irin na bude kofa ga kasashen waje, tare kuma da inganta dokokin shari'a da suka shafi hulda da kasashen waje da dokar da ta shafi jarin gida da na waje. A shekarar da ta gabata wato 2018, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wadda ita ce hukumar ikon kolin kasar, ta ayyana dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa a shirin kafa dokoki na shekarar, wadda ta zama dokar tushe da ta shafi zuba jarin da baki 'yan kasuwa suka yi a kasar Sin. Haka kuma dokar ta maye gurbin wasu dokokin jarin waje uku na yanzu, wadanda suka hada da "dokar kamfanonin hadin-gwiwar jarin gida da waje", da "dokar kamfanonin jarin waje", gami da "dokar kamfanonin da Sin da kasashen waje suka kafa tare".
Daftarin dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa na hade da wasu ayoyi shida, ciki har da babbar manufa, da sa kaimi ga zuba jari, da kiyaye zuba jari, da sa ido kan zuba jari, da nauyin doka da kuma wasu karin manufofi. Wannan doka na da babbar ma'ana, wadda ta maida martani ga tambayoyin kasashen waje, da kuma shaida irin niyyar kasar Sin ta fadada bude kofarta ga kasashen waje.
Manazarta sun nuna cewa, an kafa dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa ne da nufin tabbatar da babban tsari da dokoki ga jarin waje a fannonin ba da iznin shiga kasuwar kasar Sin, da ingantawa da kiyayewa da kuma tafiyar da harkoki a fannin, kana yayin da baki 'yan kasuwa ke gamuwa da matsala a nan kasar Sin, za su iya warware matsalar ta hanyar dokokin da abin ya shafa cikin adalci. Game da ayar dake cikin dokar ta "kafa tsarin binciken tsaron zuba jari na baki 'yan kasuwa, don tantance jarin waje da mai yiwuwa ko zai kawo illa ga tsaron kasar", wannan ya nuna 'yancin kan kasar Sin ne kuma ya dace da ka'idodjin da kasashe daban daban suke bi. Tuni dai aka kafa irin wannan tsari a kasar Amurka da kasashe mambobin kungiyar EU, kuma a shekarun nan su kan gudanar da tsarin ne cikin tsanani. Don haka, wanna ba abun mamaki ba ne.
Ana sa ran zartas da dokar a taron majalisar wakilan jama'ar kasar na wannan karo, kuma za ta maye gurbin dokoki uku game da jarin waje da aka gudanar a da, kana za ta nuna cewa, kasar Sin na kara mai da hankali kan bude kofa a fannin dokoki. Bisa yanayin da ake ciki na fuskantar rashin tabbas kan tattalin arzikin duniya a bana, kasar Sin ta tabbatar da zaman karko a fannonin siyasa da zaman al'umma, kuma tana da babbar kasuwa mai inganci, baya ga haka tana da wani cikakken tsarin masana'antu. Don haka, ana sa ido da ganin dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa za ta taimakawa baki 'yan kasuwa don su kara samun saurin ci gaba, da kuma ba da tabbaci ga kasar Sin wajen kara samun ci gaba mai inganci da kara bude kofa ga gasashen ketare bisa babban matsayi. (Sanusi Chen, Murtala Zhang, Bilkisu Xin)