in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya bayyana manufofin kasar kan harkokin dimplomasiyya
2019-03-08 16:41:32 cri

Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar Sin kuma mamban majalisar gudanarwar kasar ya kira taron manema labarai a yau Jumma'a a birnin Beijing, inda ya amsa tambayoyin da manema labarai na gida da na waje suka yi masa kan manufofin kasar Sin kan harkokin diplomasiyya da dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen waje. A yayin taron na tsawon sa'o'i biyu, Mr. Wang Yi ya sha bayyana cewa, kasar Sin na son yin kokari tare da kasashe daban daban wajen kiyaye tsarin kasancewar bangarori da dama da ma kundin tsarin MDD da dai sauran tsare-tsaren duniya.

Bana shekara ce ta cika shekaru 70 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin. A cikin shekaru 70 da suka wuce, ayyukan diplomasiyya nata ya samu babban ci gaba bayan haye wahalhalu da dama, lamarin da ya sa Sin na taka muhimmiyar rawa a harkokin duniya. Wang Yi ya bayyana cewa, jagorancin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin shi ne muhimmin dalilin da ya sa Sin ta samu manyan nasarori ta fuskar diplomsiyya, wanda ya bada tabbaci sosai a siyasance. Wang ya kara da cewa,

"A cikin wadannan shekaru 70 da suka gabata, Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin tana ta kyautata tsarin ka'idojin diplomasiyya na kasar bisa halin da ake ciki, har ma ta samu kyawawan al'adu da halin musamman nata. A shekarar 2018, an tabbatar da matsayin jagorancin tunanin Xi Jinping kan harkokin diplomasiyya, lallai wannan wani babban sakamako ne mai ma'ana a tarihin raya ka'idojin diplomasiyya na Sin. Tunanin kuwa ya zama babbar ka'idar Sin wajen raya harkokin waje, da ma warware matsaloli masu sarkakiya dake damun duniya a halin yanzu."

Za a kira taro na biyu na dandalin tattaunawar hadin kan kasa da kasa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" a karshen watan Afrilun bana a birnin Beijing. Mr. Wang Yi ya bayyana cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci bikin bude taron da kuma bada jawabi, sa'an nan zai shugabanci taron shugabanni a yayin taron. Game da halin musamman na taron, Wang ya furta cewa,

"wannan taron na biyu na da halin musamman guda uku, wato na farko, yawan shugabannin kasashe da za su halarci taron ya zarce na bara. Na biyu, wakilai fiye da 1000 daga kasashe fiye da 100 za su halarci taron. Na uku, za a shirya tarukan tattaunawa 12 a yayin taron, sannan za a kira taron 'yan kasuwa na farko domin samar da dandali ga hadin gwiwar masana'antu da kasuwanci."

Game da dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, Wang Yi ya yi tsokacin cewa, bana shekara ce ta cika shekaru 40 da kafa huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Amurka. Yadda za a sa kaimi ga ci gaban dangantakar sassan biyu bisa tushen samun daidaito da hadin kai da ma kwanciyar hankali, wani muhimmin ra'ayin bai daya ne da shugabannin kasashen biyu suka cimma, wanda kuma ya kamata ya zama babbar ka'idar da sassa daban daban na kasashen biyu za su bi. Wang yana mai cewa,

"Darasin da muka samu shi ne, hadin gwiwar zai amfanawa juna, rikici yana raunana juna. Idan aka kara tinzira juna, to za a rage damar hadin kansu. Don haka muna fatan Amurka za ta iya yin watsi da ra'ayin yin takara ba tare da hadin kai ko kadan ba, da yin kokari tare da Sin domin inganta hadin kansu yayin da suke yin takara yadda ya kamata, ta yadda za su samu moriyar juna yayin da suke raya kansu." (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China