190306-Aliyu-Usman-Bakori.m4a
|
A jiya ne, aka kaddamar da taro na biyu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 a birnin Beijing, inda firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar da rahoton aikin gwamnati na bana. Wakilinmu Ahmad Inuwa Fagam ya zanta da jakada na biyu a ofishin jakadancin Najeriya dake Sin, Ambasada Aliyu Usman Bakori, inda ya ce rahoton aikin gwamnati da Li Keqiang ya gabatar na da babbar ma'ana, kuma irin ci gaba da dimbin nasarorin da kasar Sin ta samu musamman a fannin kawar da fatara abun a yaba ne. Ambasada Aliyu Bakori ya kuma yi bayani kan hadin-gwiwa da kyakkyawar alakae dake tsakanin kasar Sin da tarayyar Najeriya.