in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manufar Sin ta ingiza ci gaban kasar, in ji masaniyar Zimbabwe
2019-03-07 13:20:14 cri

A cikin 'yan kwanakin nan, muhimman taruka biyu wato taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da taron majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar sun jawo hankalin masanan kasashen dake kudancin nahiyar Afirka, inda masaniyar kasar Zimbabwe Fay King Chung tana ganin cewa, har kullum kasar Sin tana kyautata manufofin da take aiwatarwa domin biyan sabbin bukatu a sabon yanayin da take ciki, tare kuma da ciyar da bunkasuwar kasar yadda ya kamata.

Yayin intabiyun da wakilinmu ya yi mata, madam Fay King Chung, ta bayyana cewa, tun bayan da aka kafa sabuwar kasar Sin a shekarar 1949 wato kafin shekaru 70 da suka gabata, sai dai tana sanya kokari matuka domin kyautata tsarin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin, musamman ma tun bayan da aka kammala cikakken taro na uku na kwamitin tsakiya na 18 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a nan birnin Beijing a shekarar 2013, gwamnatin kasar ta kara sanya kokari domin zurfafa aikin kwaskwarima a cikin kasar daga dukkan fannoni domin biyan sabbin bukatu a sabon yanayin da take ciki, ta yadda zata ingiza ci gaban kasar a bangarori daban daban, duk wadannan sun samar da abin koyi ga kasashen Afirka yayin da suke kokarin raya kasashensu, tana mai cewa, "Idan aka kwatanta yanayin da kasashen duniya ke ciki a shekarar 1949 da shekarar 1978, da gaske akwai bambanci matuka, ba ma kawai kasar Sin ta yi manyan sauye-sauye bane, har ma daukacin kasashen duniya su ma sun yi manyan sauye-sauye, a don haka ya zama wajibi a tsara manufofin da suka dace da sabon yanayin da ake ciki, kasar Sin ita ma ta yi hakan, musamman ma a cikin shekarun baya bayan nan, kasar Sin ta yi gyaran fuska a fannoni daban daban, misali kan tsarin tattalin arazikin kasar, yanzu haka kasar Sin ta kara maida hankali kan ci gaban kimiyya da fasaha da kuma masana'antun kere-kere."

Madam Fay Chung ta dauka cewa, ci gaban kasar Sin shi ma ya samar da damammaki ga kasashen Afirka, hakika ci gaban kasar Sin ya riga ya sa kaimi kan ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma a wurare daban daban na kasashen Afirka, ta ce, "Na ga ci gaban kasar Sin ya sa kaimi kan ci gaban kasashen Afirka, misali a fannin samar da manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, kasar Sin ta samar da taimakonta kan aikin gina filin jiragen sama da hanyar mota, da layin dogo, kana da fannin sadarwa, kamfanonin kasar Sin kamar su Huawei da sauransu sun taimakawa kasashen Afirka matuka, ban da haka kuma, kasar Sin ita ma ta samar da tallafinta kan aikin kere-kere na kasashen Afirka, misali a kasar Zimbabwe, manoma sama da miliyan biyu suna bukatar injunan aikin gona, a don haka kasar Sin ta samar musu injuna masu inganci da farashi mai araha, lamarin da ya daga matsayin kasarmu wajen raya aikin gona ta hanyar yin amfani da injunan zamani."

Masaniyar ta kara da cewa, bisa aiwatarwar shawarar ziri daya da hanya daya, hadin gwiwar dake tsakanin shiyya shiyya kamar su hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka zai kara karfafuwa sannu a hankali, hakan kuma zai kara karfin raya kasa a tsakanin bangarorin, ta ce, "Ina ganin cewa, a halin da ake ciki yanzu, ana aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya lami lafiya, a don haka hadin gwiwar dake tsakanin shiyya shiyya shima yana kara karfafuwa sannu a hankali, kana kara karfafuwa hadin gwiwar dake tsakanin shiyya shiyya zai ingiza ci gaban hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, duk da cewa, kila ne kara habaka cudanyar tattalin arzikin duniya zai gamu da matsala, amma hadin gwiwar dake tsakanin shiyya shiyya da kuma hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu zasu kara karfafuwa, kasar Sin ta riga ta samu babban sakamako yayin da take gudanar da hadin gwiwar dake tsakanin shiyya shiyya, wato kasar Sin ta zuba jari da dama a kasashen dake Asiya da tekun Pasifik da kasashen Afirka da kuma nahiyar Amurka ta kudu, domin gudanar da hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu a fannonin gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a da samar da makamashi da gudanar da harkokin cinikayya, a bayyane ne an ga sassan biyu sun samu moriyar juna mai faranta rai."

Madam Fay Chung ta taba zama ministar bada ilmi ta Zimbabwe, wadda ita ce ministan kasar 'yar asalin kasar Sin daya kacal a tarihi, yanzu haka ita ce shugabar jami'ar matan Afirka.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China