in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na da kyakkyawan fata game da tattaunawar cinikayya dake tsakaninta da Amurka
2019-03-09 17:01:35 cri
Mataimakin Ministan harkokin cinikayya na kasar Sin, Wang Shouwen, ya ce yana da kyakkyawan fata game da makomar tuntubar juna da ake yi tsakanin kasar Sin da Amurka kan tattalin arziki da cinikayya.

Wang Shouwen, wanda kuma shi ne mataimakin wakilin kasar Sin dake jagorantar tattaunawar Sin da Amurka, ya ce ayarin kasashen biyu na iyakar kokarinsu wajen aiwatar da matsayar da shugabanninsu suka cimma.

Kawo yanzu ayarin kasashen sun gudanar da zagaye na 3 na tattaunawa cikin sama da watanni 3.

Wang Shouwen, ya ce cimma yarjejeniyar moriyar juna abu ne da ya dace da muradun kasashen biyu da ma duniya baki daya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China