Yayin wani taron manema labarai, a gefen taron wakilan jama'a na kasar Sin, ministan harkokin cinikayya na kasar Zhong Shan, ya ce ma'aikatarsa zata aiwatar da matakan saukaka cinikayya da wasu matakai na inshora da samar da kudin fitar da kayayyaki, da sauransu, domin rage matsi da kuma karawa kamfanonin dake hulda da kasashen waje inganci.
Ya kara da cewa, za kuma a matse kaimi wajen inganta yanayin kasuwanci domin karawa kamfanon kwarin gwiwa.
Ya ce kasar Sin za ta inganta hadin gwiwa da kasashen waje karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, da kuma lalubo sabbin kasuwanni yayin da take kara inganta tsoffi.
Ministan ya ce cinikayyar kasar Sin na wani babban mataki, sai dai har yanzu matakinsa na gogayya bai kai yadda ake so ba, yana cewa ma'aikatar za ta karfafa fitar da manyan kayayyakin fasa masu inganci da daraja.
A cewarsa, za a fadada shigo da kayayyaki cikin kasar domin cimma bukatu na cikin gida. (Fa'iza Msutapha)