in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya jaddada bukatar juriya kan yaki da talauci
2019-03-07 20:16:12 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya yi kira da a kara juriya a yakin da ake yi da talauci, ganin shekaru biyu kacal suka ragewa kasar ta cimma burinta na kawar da kangin talauci nan da karshen shekarar 2020.

Xi wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS kana shugaban rundunar askarawar kasar, ya bayyana haka ne yayin da ya halarci zaman tattaunawa da wakilai daga lardin Gansu a zama na biyu na taron majalisar wakilan jama'a na 13 dake gudana yanzu haka a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Shugaba Xi ya ce, bai kamata a gaji ba, har sai an cimma wannan nasara baki daya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China