Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya yi kira da a kara zage damtse wajen aiwatar da dabarun raya yankunan karkara, ta yadda za a cimma manufar zamanantar da aikin gona da yankunan karkara.
Xi wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS kana kwamandan askarawar kasar, ya yi wannan kiran ne, lokacin da yake tofa albarkacinsa yayin da ya halarci zaman tattaunawa da wakilai daga lardin Henan, a zama na biyu na taron majalisar wakilan jama'a karo na 13 dake gudana a halin yanzu a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Xi ya ce, babban jigon aiwatar dabarun raya yankunan karkarar, shi ne tabbatar da cewa, an samar da amfanin gona mai muhimmanci, musamman hatsi. (Ibrahim)