in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta bukaci a bi sannu a hankali kan janye dakarun wanzar da zaman lafiya a Somalia
2019-02-19 10:24:34 cri
Kungiyar tarayyar (AU) ta yi kira da a bi sannu a hankali game da shirin janye dakarun wanzar da zaman lafiya na AU dake aiki a Somaliya wato (AMISOM).

Jami'in majalisar zaman lafiya da tsaro na AU shi ne yayi wannan kiran a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin a lokacin taro na baya bayan nan da aka gudanar domin amincewa da yarjejeniyar ayyukan zaman lafiya ta (CONOPs) na ayyukan dakarun AMISOM na shekarar 2018 zuwa 2021.

A watan Nuwambar shekarar da ta gabata, AMISOM ta tsara wani daftari wanda zai samar da wani tsarin sauya fasalin ayyukan tsaro da nufin mayar da alhakin tafiyar da tsaron daga hannun AU zuwa dakarun tsaron kasar Somaliya.

Sabuwar yarjejeniyar, wadda ke tafiyar da ayyukan AMISOM a tsawon wa'adin aikinta tsakanin 2018-2021, zai kawo karshen wa'adin aikin tawagar tsaron ta AU, inda za ta fice baki daya daga kasar ta Somalia.

A kudirin dokar kwamitin sulhun MDD mai lamba 2431 wanda aka amince da shi a shekarar 2018, ta bukaci a rage adadin dakarun tsaron, bayan rage adadin dakarun na farko da aka gudanar a watan Disambar 2017. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China