Quartey ya bayyana hakan ne a lokacin ganawa da daraktan cibiyar kungiyar hadin gwiwar raya tattalin arziki da bunkasa ci gaba (OECD) Mario Pezzini, a helkwatar kungiyar tarayyar Afrika dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, inji sanarwar kungiyar ta AU.
Yayin tattaunawarsa da Pezzini, Quartey, ya jaddada muhimmancin kara yin hadin gwiwa tsakanin kungiyar AU da cibiyar raya ci aba ta OECD, musamman a bangarorin da suka shafi bincike da kididdiga a Afrika.
A cewar Quartey, muhimman abubuwan da kungiyar AU ta fi mayar da hankali sun hada da, amfani da kimiyya da fasaha a Afrika da nufin kyautata zaman rayuwar al'ummomin nahiyar.(Ahmad Fagam)