#2019Taruka2# Yawan sabbin kamfanoni masu jarin waje da aka kafa a kasar Sin ya karu da kusan 70% a bara
A cikin rahoton gwamnatin kasar Sin, Li Keqiang ya sanar da cewa, a shekarar 2018, kasar Sin ta bude kofarta daga dukkan fannoni, matsayin da take dauka na kara kyautata yanayin kasuwanci ya daga sosai a duk duniya, sannan shawarar "Ziri daya da hanya daya" ta samu ci gaba sosai. Bugu da kari, yawan jarin waje da aka yi amfani da su ya kai dalar Amurka biliyan 138.3, wato yana kan sahun gaban sauran kasashen duniya. Dadin dadawa, yawan harajin kwastam da kasar Sin ta buga kan kayayyakin da ake shigowa ya ragu daga 9.8% zuwa 7.5%. Sannan kuma, kasar Sin ta bude kofarta a fannonin da suke da alaka da hada-hadar kudi da motoci, sabo da ta rage yawan sana'o'in da ake hana baki 'yan kasuwa zuba jari a ciki. Har ma an kaddamar da wasu manyan ayyukan jarin waje a kasar. Sakamakon haka, a bara, yawan sabbin kamfanoni masu jarin waje da aka kafa a kasar Sin ya karu da kusan 70%. (Sanusi Chen)