Matakan sun hada da karfafa aikin kyautata rayuwar jama'a, ankarar da hukumomi masu zaman kansu, da masu aiki sa kai, da daidai jama'a masu bada tallafi da su shiga cikin shirin gangamin yaki da fatara, da saukakawa mutane masu bukata ta musamman, da samar da kyakkyawar kulawa ga tsofaffi da yara marasa galihu a yankunan karkara, da kuma kyautata ayyukan gwamnatoci na kananan yankuna ga al'ummominsu da kuma gyara dukkan kura-kurai.
Minista mai kula da harkokin jin dadin al'umma Huang Shuxian, shi ne ya bayyana hakan a yayin wani taron kasa ta kafar bidiyo, inda ya bukaci jami'an ma'aikatar kula da jin dadin al'umma a dukkan matakai da su kara kaucewa duk wasu hanyoyi da suka shafi rashawa kuma su inganta kwarewarsu da bin ka'idoji a lokacin gudanar da ayyukansu.
Mahukuntan kasar Sin sun yi alkawarin tabbatar da samun nasara a aikin yaki da talauci cikin kasa da shekaru 3 masu zuwa. A bisa tsarin hukumomin kasar Sin, ya zuwa shekarar 2020, za'a tsame dukkan mazauna karkara daga cikin kangin fatara. (Ahmad Fagam)