in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kara azama don yaki da fatara
2019-02-21 10:44:24 cri

Kasar Sin ta cimma muhimmiya kuma gagarumar nasara a shirinta na yaki da fatara cikin shekaru 6 da suka gabata, kuma za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka a cikin wannan shekarar domin kafa wani muhimmin tsari da zai baiwa kasar nasarar yakin da take da fatara nan da shekarar 2020, wani jami'in kasar ne ya bayyana hakan.

A shekaru shida da suka gabata, kasar Sin ta tsame mazauna karkara miliyan 82.39 daga kangin fatara, daga cikin jimillar matalautan dake zaune a yankunan karkara miliyan 98.99 a kasar zuwa karshen shekarar 2012, adadin ya koma miliyan 16 zuwa karshen shekarar bara, Ou Qingping, mataimakin daraktan hukumar yaki da fatara ta kasar, ya bayyana hakan ne ga manema labarai.

Alkaluman talauci ya ragu daga kashi 10.2 zuwa kasa da kashi 1.7 bisa 100, in ji Ou.

Shekarar bana tana da muhimmanci saboda aka sa ran kawo karshen shirin yaki da fatara da aka tsara zuwa shekarar 2020, inda ake fatan tsame mazauna karkara miliyan 10 daga kangin fatara.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China