in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu saurin ci gaba ta fannin saukaka fatara a sassan dake matukar fama da talauci na kasar Sin
2018-12-23 16:21:47 cri
Sassan dake matukar fama da talauci a kasar Sin sun samu saurin ci gaba ta fannin saukaka fatara a shekarar 2018.

Mr. Liu Yongfu, darektan ofishin kula da ayyukan saukaka fatara da ci gaba na majalisar gudanarwa ta kasar ne ya fadi haka, kuma ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin da kananan hukumomin kasar sun kaddamar da manufofi na kara samar da tallafi ga sassan dake fama da talauci a duk fadin kasar, kuma "shirye-shiryen da abin ya shafa ya gudana kamar yadda aka shirya, har ma tuni an kammala wasu kafin lokacin da aka tsara".

Mr. Liu ya kara da cewa, a mataki na gaba, kasar Sin za ta maida hankali a kan daidaita matsalolin da suka sanya al'umma cikin talauci, kuma matakan da za a dauka sun hada da samar da guraben aikin yi da kuma kaddamar da manufofi na tallafawa masu karamin karfi.

Tun bayan shekarar 1978, kasar Sin ta fidda al'umma miliyan 740 daga kangin talauci, hakan nan ya rage kason al'umma dake fama da talauci da kashi 94.4%. Kasar ta kuma lashi takobin fidda gaba dayan al'ummar da ke fama da talauci a karkara daga halin da suke ciki ya zuwa shekarar 2020. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China