A kwanakin baya ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bada umurni game da harkokin yankin gwaji na Bijie dake lardin Guizhou, inda ya jaddada cewa, sakamakon jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar, da goyon-bayan bangarori daban-daban, gami da kwazon da jama'a suka nuna, an samu manyan sauye-sauye a yankin Bijie, har ya zama wani abun misali ga yankuna masu fama da talauci don su cimma nasarar yaki da talauci.
Shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata a zage damtse don tabbatar da ganin an cimma nasarar yaki da talauci cikin lokaci a yankin gwaji na Bijie. Har wa yau, ya zama dole a yi hangen-nesa da bullo da wasu shirye-shirye, don neman samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, da tsare-tsare da yin kirkire-kirkire a yankin gwaji na Bijie.(Murtala Zhang)