Hukumar kula da ayyukan zirga-zirgar jiragen saman fasinjoji ta kasar Sin ta ba da rahoton aiki na filayen jiragen saman fasinja na shekarar 2018 a ranar 6 ga wata, inda aka nuna cewa, a bara, yawan filayen jiragen saman fasinja ya kai 235, yayin da yawan fasinjojin da aka yi jigilarsu ya zarce biliyan 1.2. Yawan filayen jigaren saman da yawan fasinjojin da suka yi jigilarsu ya zarce miliyan 10 ya kai 37.
Rahoton kuma ya bayyana cewa, yawan fasinjojin da filin jirgin sama na birnin Beijing ya yi jigilarsu ya zarce miliyan 100 a bara, wanda ya zama na farko a cikin dukkan filayen jiragen saman na Sin.(Kande Gao)