in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kara zuba jari a bangaren jiragen sama a shekarar 2019
2019-01-08 10:21:31 cri

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Sin (CAAC) ta bayyana cewa, a shekarar 2019 kasar tana fatan kara yawan jarin da ya kai Yuan biliyan 85, kwatankwacin dala biliyan 12.41 a wannan bangare.

Shugaban hukumar ta CAAC Feng Zhenglin shi ne ya bayyana hakan yayin wani taron aiki da hukumar ta shirya. Ya ce, ana sa ran ribar da sashen ke samu za ta karu zuwa kaso 11.8 cikin 100 bisa makamancin lokaci na bara. Haka kuma yawan jigilar fasinjoji da ta kayayyaki za ta karu da kaso 11 cikin 100 yayin da jigilar wasiku ita ma za ta karu da kaso 5.7 cikin 100 bisa makamancin lokaci na bara.

Feng ya ce, a shekarar da ta gabata sashen zirga-zirgar jiragen saman kasar ya ba da gagarumar gudummawa, inda aka samu ribar da ta kai kaso 11.4 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata .

A shekarar 2018, an bude sabbin hanyoyin jiragen saman kasa da kasa guda 167, kuma 105 daga cikin wannan adadi suna kai komo tsakanin birane da suka shiga shawarar ziri daya da hanya daya. Kimanin hanyoyi 4,206 da jiragen kasar Sin ke kai komo. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China