in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi gwajin jirgin sama dake iya tafiya a ruwa
2018-08-27 09:59:44 cri
Kamfanin kirar jiragen sama mallakar kasar Sin, ya bayyana nasarar da ya cimma, ta gwajin jirgin sama dake iya tafiya a ruwa irin sa na farko da kamfanin ya kera.

Jirgin mai lamba AG600, ya kammala gwaji a sama, ya kuma shiga zangon farko na gwajin aiki a kan ruwa. Kamfanin ya ce AG600, ya kammala gwanin tashi ne daga birnin Zhuhai na lardin Guangdong dake kudancin kasar ta Sin, inda ya isa filin jiragen sama na Jingmen, dake lardin Hubei a tsakiyar kasar.

Tuni dai jirgin ya kammala gwaje gwaje daban daban, tun fara auna ingancin aikin sa a watan Disambar bara. Yanzu kuma ana fatan ci gaba da gwada ingancin sa a ruwa a birnin Jingmen.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China