Darajar kwangilolin da aka kulla a bikin baje kolin kayayyakin jiragen sama na shekarar 2018 ya wuce dalar Amurka biliyan 20

A yamamcin jiya Lahadi 11 ga watan, aka rufe baje kolin kayayyakin jiragen sama da kasa da kasa karo na 12 da aka shirya a birnin Zhuhai na kasar Sin, inda aka kulla yarjejeniyoyi da takardun neman yin hadin gwiwa 569 da darajarsu ta kai sama da dalar Amurka biliyan 21.2, ciki har da jiragen sama iri iri 239 da ake son saya.
Rahotanni na cewa, a cikin kwanaki 6 na baje kolin, kamfanoni da sana'o'i 770, ciki har da kamfanoni 350 daga kasashe da yankuna 43 sun halaci baje kolin. (Sanusi Chen)