in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kaddamar da sabon samfurin jirgin dakon kayan sama jannati a 2019
2018-04-27 10:30:50 cri

Wani kamfanin kera na'urorin sufurin sama jannati dake birnin Wuhan a lardin Hubei dake nan kasar Sin, ya sha alwashin kaddamar da aikin wani jirgin saman dakon kayayyakin sama jannani na zamani, nan da shekara mai zuwa.

Shugaban hukumar gudanarwar kamfanin Lyu Dongming, ya ce za a yi gwajin wannan samfuri na jirgi ne a shekara mai zuwa, zai kuma kunshi sabbin fasahohi da za su ba da damar aiki da shi cikin sauki da kuma araha.

Mr. Lyu Dongming ya kara da cewa, za a kera jirgin ne da wasu sassa masu inganci, dake tattare da fasahohin kare shi daga hadurra, da yanayi wanda zai inganta aikin sa na kai kayayyakin sama jannati inda ake bukatar su, da kuma yiwuwar dawowar su doron duniya ba tare da wata tangarda ba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China