Mai kafa asusun kare namun daji na Mara Xing Ba ya bayyana cewa, an samar da motoci, da baburori, da tantuna, da mabudi mai hangen nesa, da na'urorin jagorancin zirga-zirga ta hanyar tauraron dan Adam na GPS da sauransu ga yankunan kare namun daji a kasar don nuna goyon bayansu da inganta karfin yaki da farautar dabbobi ba bisa ka'ida ba. Za a samar da baburori ga yankuna 8 zuwa 10 na kasar Kenya.
Kungiyar kare namun daji ta gabashin Afirka tana daya daga cikin manyan kungiyoyin kare namun daji ta nahiyar Afirka. Asusun kare namun daji na Mara shi ne kungiyar jin dadin jama'a mai zaman kanta ta farko da dan kasar Sin ya kafa a nahiyar Afirka, bisa nufin sa kaimi ga yin nazari da kare dabbobin irin na Felidae. (Zainab)