in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 2 sun jikkata a sanadiyyar fashewar wani abu a babban birnin kasar Kenya
2019-01-27 16:10:11 cri
A kalla mutane biyu ne suka samu raunuka yayin da wasu abubuwan fashewa suka tarwatse a wani titi mai yawan zirga-zirgar jama'a a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, da yammacin jiya Asabar, hukumomin 'yan sandan kasar sun tabbatar faruwar lamarin.

Kwamandan hukumar 'yan sandan birnin Nairobi, Philip Ndolo ya ce, wani keke tura kaya da wani mutum da ba'a san kowane ne ba ya karbi hayarsa domin dibar jakankunansa a tsakiyar birnin yana dauke da abubuwan fashewa a cikinsa, ya yi matukar jikkata mutumin dake tura kayan. Da kuma wani mutumin dake wucewa ta kusa da inda lamarin ya auku shi ma ya samu kananan raunuka.

'Yan sanda sun garzaya da wadanda suka jikkatan zuwa asibiti. "Akwai kuma masana kan boma bomai a wajen," in ji Ndolo.

Mai tura keken daukar kayan ya ce, kayan sun fashe ne mintoci 10 bayan da mutumin da ya dauki hayar tasa ya tafi wani waje da nufin dauko katinsa na shaida wanda ya yi ikirarin cewa ya manta da katin nasa. Ya bayyana hakan ne ga 'yan jaridu bayan an garzaya da shi asibitin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China