in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Antonio Guterres ya yi Allah wadai da harin ta'addanci na birnin Nairobi
2019-01-16 10:11:48 cri

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi matukar Allah wadai da harin ta'addancin da aka kaddamar a birnin Nairobin kasar Kenya, wanda ya hallaka mutane a kalla shida, tare da jikkata wasu da dama.

Da yake tabbatar da hakan, kakakinsa Stephane Dujarric, ya ce Mr. Guterres ya bayyana goyon bayan sa ga al'umma da gwamnatin kasar ta Kenya, kan wannan al'amari da ya same su.

Rahotanni ne cewa, mayakan kungiyar al-Shabab ne suka kaddamar da hare-hare, kan wani otel dake hade da wata kasuwa, da kuma wani rukunin ofisoshi a birnin na Nairobi. An ce maharan na dauke da bindigogi da gurneti, an kuma ji wata karar fashewa yayin da suka farwa ginin.

A wani ci gaban kuma, gwamnatin Kenya ta ce jami'an tsaro sun shawo kan yanayin da ake ciki a birnin, bayan harin na jiya Talata. A cewar sakataren ma'aikatar cikin gida da tsare-tsaren gwamnatin kasar Fred Matiang'i, tuni aka tura dakarun tsaro domin kwashe 'yan kasar Kenya dake cikin harabar ginin, bayan shafe sa'o'i 9 ana daukar matakai na tsaro.

Fred Matiang'i, ya ce yanzu haka daukacin 'yan kasar da masu kai ziyara, na da cikakken tsaro, don haka ya kamata kowa ya kwantar da hankalin sa. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China