in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan wadanda suka rasu yayin harin kasar Kenya ya kai mutum 21
2019-01-17 09:35:26 cri
Rundunar 'yan sanda a Kenya ta ce ya zuwa ranar Talata, yawan mutanen da harin birnin Nairobi ya rutsa da su ya kai mutum 21, bayan da aka gano karin wasu gawawwaki 6, kana wani dan sanda dake jinya ya rasu a asibiti.

Babban sifeton 'yan sandan kasar Joseph Boinnet, ya bayyanawa wani taron manema labarai cewa, dan sanda daya da ke cikin rundunar da ta yi dauki ba dadi da 'yan ta'addan ya rasu a asibiti, kana an gano karin mutum shida da su ma suka rasu sakamakon artabun.

Kaza lika a cewar jami'in, mutane 28 na samun kulawar jami'an lafiya a asibitoci daban daban dake birnin Nairobi. Ya kuma ce yayin fafatawar, an hallaka 'yan ta'addan biyar.

Sifeton 'yan sandan ya ce mutum 21 da suka rasu yayin harin, sun kunshi mutane 16 'yan asalin kasar, da dan Birtaniya daya, da Ba'amurke daya, da kuma wasu 'yan kasashen Afirka uku, wadanda ba tantance su wane ne ba.

Joseph Boinnet ya kuma ce binciken da sashen nazarin manyan laifuka na rundunar ya gudanar, ya ba da damar cafke wasu da ake zargi da hannu cikin kitsa harin su 2, inda kuma suke ci gaba da tallafawa binciken da ake yi. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China