Kenyatta ya bayyana ta kafar talabijin cewa, an kawo karshen matakan tsaron da aka kaddamar kana an kashe dukkan 'yan ta'addan da suka kai hari a harabar otel din DusitD2, lamarin da ya kawo karshen sa'o'i 18 na harin ta'addancin da aka kai a babban birnin kasar.
Shugaban ya kuma lashi takobin karfafa matakan yaki da ayyukan ta'addanci a duniya, yana mai cewa, 'yan ta'adda ba za su taba samun galaba a kan mu ba.
Rundunar 'yan sandan kasar Kenya ta bayyana cewa, 'yan ta'adda shida ne suka kaddamar da harin. Kungiyar 'yan ta'adda ta al-Shabaab dake Somaliya ta dauki alhakin kaddamar da harin.(Ibrahim)